OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Sanda Sun Ceto Mutum Uku Da Kashe Wanda Suka Yi Garkuwa Da Su a Bauchi

'Yan Sanda Sun Ceto Mutum Uku Da Kashe Wanda Suka Yi Garkuwa

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta samu nasarar ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Toro ta jihar.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma kashe biyu daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su a yayin aikin ceton.

Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil ne ya tabbatar da hakan a Bauchi.

Wakil ya kara da cewa rundunar ta samu rahoto a ranar 26 ga watan Agusta cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wani Alhassan Gambo na Anguwan Bawa na jihar Kaduna tare da harbe wani Mujitafa Usman na karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.

Masu garkuwa da mutanen sun tare hanyar Tulu zuwa Rishi a karamar hukumar Toro kafin su gudanar da aika-aikan. 

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin dan kasuwa ne da ya kai ziyarar kasuwancin sa. 

A cewar Wakil: “A ranar 28 ga watan Agusta, an bada sahihan bayanan sirri ga hedikwatar ‘yan sandan Tulu kan ayyukan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

“Tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda reshen Tulu, da ‘yan banga, sun shiga aikin binciken yankin.

“A ranar 29 ga watan Agusta, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka hadu a tsaunin Doka Auwalu da ke unguwar Tama a karamar hukumar Toro, inda suka yi artabu da ‘yan sanda.

“Bayan zazzafar musayar wutar da aka yi, jami’an sun kashe biyu daga cikin wadanda ake zargin a nan take, yayin da wasu kuma suka tsere da harbin bindiga a jikin su cikin dajin.

“Abin takaici, wani dan banga ya rasu, jami’an sun yi nasarar ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da sun ji rauni ba, daga bisani kuma aka hada su da iyalan su bayan an duba lafiyar su,” inji shi.

Wakil ya ce a wani samame da rundunar ta kai ta kama wasu mutane 22 da ake zargin ‘yan daba tare da kwato makamai da kayan maye a cikin watan Agusta.

Ya kara da cewa rundunar ta samu rahoto a ranar 30 ga watan Agusta cewa wasu ‘yan bindiga dauke da wukake sun kai hari ga mambobin kwamitin zaman lafiya da tsaro a Unguwar Bakin Kura a cikin babban birnin jihar.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, Wakil ya ce: “Da samun labarin, wata tawagar jami’an tsaro karkashin jagorancin kwamandan Rapid Response Squad (RRS) ta yi gaggawar daukar mataki tare da cafke wasu maza 22 da ake zargi."

Kayayyakin da ‘yan sandan suka kwato sun hada da wukake guda hudu, kwalabe guda biyu, sanduna biyu, kakafi daya, sativa na wiwi, da alluran diazepam guda 221.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Umar Sanda ya jajantawa iyalan ‘dan banga da ya rasa ransa yayin gudanar da aikin tare da yabawa jami’an da suka yi kokarin da yasa aka samu nasarar.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci