OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan sanda sun cafke wani mutum dauke da katin zabe 101 a Sokoto

'Yan sanda sun cafke wani mutum dauke da katin zabe 101 a So

Nigerian Police force

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da cafke wani mutum mai suna Nasiru Idris da katin zabe na dindindin (PVC) guda 101 a jihar Sokoto.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a yau a Sokoto, kwamishinan ‘yan sandan, Hussain Gumel ya ce an kama wanda ake zargin ne a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar.

Ya ce bisa sahihin bayani da suka samu, jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin a ranar 10 ga watan Oktoba.

Kwamishinan ya kara da cewa yayin da aka kama wanda ake zargin bai iya bayyana yadda ya mallaki katinan ba.

A cewar sa: “An yi tsammanin cewa masu wadannan katunan ba ‘yan karamar hukumar Sabon Birni ne kadai ba, za su iya kasancewa daga sassan jihar saboda ba mu iya gano wadanda suka mallaki katinan ba.

Gumel ya kuma yi kira ga jama’a da watakila sun rasa katunan su da su zo su duba.

Ya kara da cewa rundunar za ta mayar da duk wasu katinan da ba a samu masu su ba ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta(INEC).

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci