OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hatsarin Kwale-kwale a Sokoto ya yi sanadin rayuka 15 yayin Halartar Bikin Mauludi

Hatsarin Kwale-kwale a Sokoto ya yi sanadin rayuka 15 yayin

Biyo bayan wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto, akalla mutane 15 ne suka rasa rayukan su a yayin da zasu halarci bikin Mauludi.

Lamarin da ya faru a jiya (Talata) da yamma ya sanya mutane cikin kunci. 

Rahotanni sun ce goma daga cikin wadanda lamarin ya shafa sun tsira da rayukan su.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Trust, shugaban karamar hukumar ta Shagari, Aliyu Abubakar Dantani ya ce wadanda abin ya shafa sun kai 25 daga kauyuka daban-daban ne da suka nufi wurin bikin.

A cewar sa: “Su 25 ne a cikin jirgin lokacin da jirgin ya kife amma an ceto 10 daga cikin su da ran su.

“Sun fito ne daga kauyuka hudu daban-daban, sun hadu a daya daga cikin kauyukan, daga nan suka shiga kwale-kwalen.

“Suna kan hanyar su ta zuwa wani kauye ne domin gudanar da bikin Mauludi na shekara amma kwale-kwalen ya kife kafin su isa inda za su.

"Mutane 15 ne suka nutse amma daga baya an gano gawarwakin su kuma aka binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada."

Yankin karamar hukumar ya sami jerin hadurran kwale-kwale da dama a baya.

Ku tuna cewa a shekarar 2021, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi alkawarin samar da rigunan ceto ga al’ummomin da ke bakin gaban kogi.

Da yake mayar da martani kan batun, shugaban majalisar ya ce batun "har yanzu yana kan hanya."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci