OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jihar Borno ta dauki kwansibilari 1,800 domin taimakawa wajen yakar laifuka

Jihar Borno ta dauki kwansibilari 1,800 domin taimakawa waje

Nigerian Police force

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta bayyana cewa ta dauki kwansibilari 1,800 aiki domin tallafa wa 'yansandan jihar wajen yaki da miyagun laifuka.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Abdu Umar ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

Umar wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ce a halin yanzu wadanda aka dauka suna samun horo kan aikin.

A cewar sa, sabbin ma’aikatan za a tura su ne zuwa kananan hukumomi 27 na jihar.

Ya kara da cewa an dauki wannan mataki ne domin inganta aikin ‘yan sanda a jihar.

Da yake karin haske, kwamishinan ya ce shirin daukan kwansibilarin na rundunar ‘yan sanda aikin sa kai ne kawai da gwamnatin tarayya ta bullo da shi.

Ya kara da cewa ayyukan ‘yan sandan sun hada da taimaka wa ‘yan sanda wajen gano laifuka da rigakafin su, magance rikice-rikice, tattara bayanan sirri da mara wa kwamandojin ‘yan sanda na yankin.

A cewar kwamishinan: “Tuni mun baza jami’an ‘yan sanda 10 a dukkan kananan hukumomin jihar domin taimaka wa sauran jami’an tsaro da ke yaki da ta’addanci da sauran laifuka.

“Ba da jimawa ba, za ku ga ‘yan sanda a ko’ina.

"Waɗannan za su sa tufafin baƙi da baƙi; sun bambanta da 'yan sandan mu a jikin aninin su da bajin su."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci