OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Daba a Zamfara Sun Shiga APC Yayin Da Suka Rungumi Zaman Lafiya

'Yan Daba a Zamfara Sun Shiga APC Yayin Da Suka Rungumi Zama

Wasu gungun 'yan daban siyasa a jihar Zamfara sun rungumi zaman lafiya tare da yin kira ga gwamnati da ta tallafa musu wajen bayar da gudunmawar ci gaban jihar.

Kungiyoyin sun ce sun yi nadamar yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da su wajen kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Kungiyoyin da ke karkashin wani Baba Karami da Garba Lawal sun ce za su mara wa gwamnati baya domin ganin an dawo da zaman lafiya a jihar yayin shigar su jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Yusuf Idris ya baiwa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN). 

Idris ya kara da cewa ’yan daban sun kuma mika makaman su a wani mataki na tabbatar da zaman lafiya.

A cewar sa, kungiyoyin sun samu tarba daga shugaban karamar hukumar Gusau, Babangida Abdullahi.

Shugaban ya bukace su da su kasance masu bin doka da oda tare da ba su tabbacin zama 'yan jam’iyyar APC daidai da saura ba tare da nuna bambanci ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci