OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Boko Haram 19 sun gamu da ajalin su yayin da suka kai wa sojoji hari

'Yan Boko Haram 19 sun gamu da ajalin su yayin da suka kai w

A kalla 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP goma sha tara ne suka gamu da ajalin su a lokacin da suka yi wa sojoji kwanton bauna a jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a tsakanin Kumshe da Banki na jihar a cewar wata majiya.

Wata majiyar da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce sojojin na Birged 21 ne suka dakile harin kwantan baunan a karamar hukumar Bama ta jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yan ta’addan sun tayar da wata bam kafin su yi ta harbin sojojin. 

A cewar majiyar: "'Yan ta'addan sun tayar da bam din ne tare da ci gaba da harbin bindiga wanda nan take sojojin suka fatattake su."

Sojojin sun yi nasarar kawar da 19 daga cikin 'yan ta'addan a yayin da ba'a samu asarar rayuka ba daga bangaren su (sojojin).

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci