OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Borno: ISWAP sun yi wa 'yan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe mutum 6

Borno: ISWAP sun yi wa 'yan Boko Haram kwanton bauna, sun ka

Akalla 'yan ta'addan Boko Haram shida ne 'yan ta'addan da ke da'awar kafa daular Islama a yammacin Afirka suka kashe a wani harin kwantan bauna.

Rahotanni sun ce mayakan na ISWAP sun mamaye sansanin 'yan Boko Haram da ke Gajibo, wani gari mai tazarar kilomita 95 daga arewa maso gabashin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A yayin farmakin, ISWAP sun kashe shida daga cikin 'yan ta'addan Boko Haram da suka ayyana a matsayin "kafirai".

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, wani kwararre a fannin yaki da ta’addanci kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan.

A cewar Makama, maharan sun kuma kwato bindigu kirar AK-47 guda biyar a sansanin na Boko Haram.

Ku tuna cewa a baya ISWAP ta kai hari kan sansanonin 'yan Boko Haram a fafatawar kishi dake tsakanin su tare da samun nasarori.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai