OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Watanni da suka shude

‘Yan Bindiga Sun Kashe wani Dan Kasuwa A Kano, Sun Raunata Abokin sa

‘Yan Bindiga Sun Kashe wani Dan Kasuwa A Kano, Sun Raunata

Wasu ‘yan bindiga sun harbe wani dan kasuwa mai suna Mista Ifeanyi, tare da raunata abokin sa a shagon sa da ke unguwar Sabon Gari a jihar Kano.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari a unguwar Azubros Plaza, kusa da titin Faransa, Sabon Gari Kano.

Shedun gani da ido sun ce babu wanda yasan daga inda ‘yan bindigar suka fito,maharan sun harbi wanda suko zo kashewa su kayi tafiyar su.

“Dama sun zo ne dan su kashe Ifeanyi bisa ga abin da muka fahimta.

Daga dayan bangaren titi suka zo inda suka wuce shagon sa kai tsaye.

Abokin sa suka fara harbi sannan daga bisani suka bi Ifeanyi in da ya gudu suka harbe shi har lahira sannan suka yi tafiyar su.

“Wani shaida daya bukaci a sakaya sunan sa ya ce :"Ba su taɓa kowa ba amma duk mun kidime.

An samu tsayawar al'amaru alokacin da abin ya faru.

Amma bayan sun tafi, an cigaba da hada hada a wurin duk da cewa lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa inda jama’a ke neman hanyar fita."

Wani ganau mai suna Jibrin Usman ya ce abokin marigayin wanda shi ma ‘yan bindigar sun harbe shi a hannunsa an garzaya da shi asibiti inda ake jinyar sa.

Yayin da har yanzu ba a san dalilin faruwar lamarin ba, Daily Trust ta tattaro cewa marigayin ya kasance hamshakin dan kasuwa ne a yankin kuma daya daga cikin manyan dillalan batira a kasuwar Sabon Gari.

Har yanzu dai 'yan sandan ba su ce komai ba game da faruwar lamarin .

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai