OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

‘Yan bindiga sun kashe sufeton ‘yan sanda, sun sace mutane da dama a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe sufeton ‘yan sanda, sun sace muta

Armed bandits/file copy

Biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai kan babbar hanyar Katsina zuwa Jibia a jihar Katsina, an kashe wani sifeton ‘yan sanda mai suna Idris Musa.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan bayan kashe shi sun banka wa motar sa ​​wuta tare da yin awon gaba da fasinjoji da dama.

Lamarin dai ya faru ne a unguwar Makera da ke da tazarar kilomita kadan da babban birnin jihar Katsina a safiyar ranar Litinin.

Rahotannin da ganau suka bayar na nuni da cewa an kai harin ne da misalin karfe 8:00 na safe yayin da maharan suka tare hanya suna harbe-harbe domin tsayar da motoci.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da hakan.

Isah ya ce sufeton ya mutu ne a lokacin da yake kokarin dakile harin.

Ya kuma bayyana cewa maharan sun yi wa marigayin kwanton bauna inda suka harbe shi a kurkusa. 

A cewar sa: “Sun kashe shi nan take tare da yin awon gaba da fasinjoji da dama dake wasu motocin haya daga karamar hukumar Jibia zuwa cikin garin Katsina domin gudanar da harkokin su na yau da kullum."

Kakakin ‘yan sandan ya ci gaba da bayanin cewa maharan sun kona motar marigayin inda suka tafi da fasinjoji da ba a san adadin su ba.

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci