OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Bindiga Sun Daureni Da Sarka Don Neman Kudin Fansa' - Cewar Wani DPO

'Yan Bindiga Sun Daureni Da Sarka Don Neman Kudin Fansa' - C

Jami’in ‘yan sanda da aka yi garkuwa da shi a Birnin Gwari dake jihar Kaduna, a watan Yuni, a lokacin da yake magana a wayan 'yan uwansa ta hannun yan ta'adda, ya ce an daure shi da sarka, tare da bukatar kudin fansa don a sake shi.

A wata hira da manema labarai, Musa Muhammad Gyadi-Gyadi, babban kanin jami’in da aka sace, ya ce yan ta'addan sun nemi da su biya kudi Naira miliyan 250 a matsayin kudin fansa, inda ya ce tun da farko iyalan sun tara Naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa, amma masu garkuwa da mutanen sun ce kudin abinci ne.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da CSP Mohammed Gyadi-Gyadi a safiyar ranar 27 ga watan Yuni, 2022, kimanin kwanaki 63 da suka gabata a lokacin da yake tuka mota zuwa shelkwatar yan sanda a karamar hukumar Birnin Gwari.

Ko da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na hukumar ‘yan sanda ta kasa reshen Birnin-Gwari a jihar Kaduna,  SP Olumuyiwa Adejobi, dai bai bayyana komai kan shirin hukumar su na kwato jami'in da yan ta'adda ke ci gaba da tsarewa ba.

Haka shima kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, DSP Mohammed Jalige, bai amsa kiran da manema labarai sukayi masa ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci