OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Sha Luguden Wuta Daga Sojin Sama a Kaduna

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Sha Luguden Wuta Daga Sojin Sama a

Hoto Daga: PremiumTimes

Dakarun sojin saman Najeriya sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga da dama a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne inda dakarun suka yi luguden wuta ta sama a kan sansanonin 'yan bindigan.

Hakan yazo ne kunshe cikin wata sanarwar dauke da sa hannun Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, an kashe ‘yan bindigar da ba a tantance adadinsu ba yayin samamen da sojoji suka musu kan sansanonin su ta sama.

Sanarwar ta kara da cewa, bayan bincike da bayanan sirri da aka samo, an kai hare-haren ne a wasu wuraren da aka gano a kauyukan Kauwuri da Gaude. 

A matakin farko dai, jiragen yaki sun kai hari a sansanonin ‘yan bindiga da ke yankin Kauwuri, inda aka hangi ‘yan bindiga dauke da makamai suna tserewa daga wuraren.

Jirgin mai saukar ungulu ya biyo bayan wani kutse da rokoki da igwa.

Haka kuma bayan an kai hari kan wata maboyar ‘yan bindiga da aka gano a yankin Gaude, an gano wasu da suke yunkurin fakewa a karkashin wasu bishiyoyi kana aka musu luguden wuta.

Sanarwar ta kara da cewa, "An kai harin ne kan wurin, yayin da sojojin kasa suka bi sawu tare da fatattakar 'yan bindiga da dama wadanda suka tsere daga wurin bayan harin."

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya nuna gamsuwa tare da yaba wa jami’an tsaro sosai kan ayyukan da suka gudanar.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama'a da su kai rahoto wurin jami'an tsaro muddin suka ga mutum yaje neman magani kan raunuka da suka alakantu da hare-haren.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci