OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yadda na tsere daga hannun masu garkuwa da mutane - Basarake a jihar Imo

Yadda na tsere daga hannun masu garkuwa da mutane - Basarake

Joel Udenkwo, sarkin garin Isiala Umudi, da ke karamar hukumar Nkwere ta jihar Imo, wanda aka yi garkuwa da shi ranar Juma’a, ya bayyana yadda ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, an sace sarkin ne a harabar daya daga cikin kamfanoninsa mai suna Udekings Electronics a Owerri da misalin karfe 7 na dare.

Mista Udenkwo ya tsere ne a ranar Litinin daga dajin Okwu inda masu garkuwa da mutanen suka killace shi a karamar hukumar Ikeduru a jihar, kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito.

Mista Udenkwo, wanda ya bayyana irin halin da ya shiga, ya ce ya tsere ne a lokacin da ya lura cewa cikin wadanda suke tsare da shi sun yi tatul da maye.

Rahotanni sun bayyana cewa bai fi sa’o’i 48 ba wadanda sukayi garkuwa da Joel suka nemi da danginsa su biya kudin fansa naira miliyan 200.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci