OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Sanda Sun Kama Matashin Da Ake Zargin Ya Yi Garkuwa Da Kan Sa

Yan Sanda Sun Kama Matashin Da Ake Zargin Ya Yi Garkuwa Da K

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wani matashi dan shekara 23 mai suna Edward Okache, wanda ake zargi da yin karyar an sace shi, inda ya nemi kudin fansa Naira miliyan 10 daga hannun iyayen sa.

 

Rundunar ‘yan sandan ta ce an kama Okache ne tare da wasu mutane hudu Asamoah Ernest, Isiah Uti, Ephraim Anyijor, da kuma Charity Lukpata wadanda ake zargin su na da hannu a aikata laifin.

 

Bayan samun labarin sace shi, ‘yar uwar sa, Comfort Okache, ta yi gaggawar kiran hedikwatar Mowe Divisional, inda ta sanar da cewa an yi garkuwa da kanin ta akan hanyar sa daga Calabar zuwa Legas a kusa da yankin Mowe na jihar Ogun.

 

A cewar kakakin ‘yan sanda a jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce masu garkuwa sun bukaci a biya Naira miliyan 10 kafin a sako Mista Okache.

 

Samun rahoton, ke da wuya DPO Folake Afeniforo, ya tattara jami'ai zuwa yankin.

 

Mista Oyeyemi ya ce, “Jami'an tsaro sun kewaye dajin, Sai aka hangi wanda aka sace a wani gini da ba a kammala ba tare da Asamoah Ernest, dan Ghana da Isiah Uti, inda aka daure shi hannu da kafafu. ”

 

‘Yan sanda sun ceto wanda aka sace tare da cafke mutanen biyu da aka samu tare da shi.

 

“Amma da isar su Ofishin 'Yan sanda wadanda ake zargin sun bayyana cewa wanda aka sacen shi ne wanda ya shirya komai tare da su don su yi garkuwa da shi domin a karbi kudi a hannun iyayensa don su zuba jari a harkar kasuwancin yanar gizo.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci