OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wasu ‘Yara Mata Biyu Sun Nutse A Ruwa Jihar Jigawa

Wasu ‘Yara Mata Biyu Sun Nutse A Ruwa Jihar Jigawa

Drown

Hukumar Farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wasu yara mata biyu da suka nutse a wasu kauyuka biyu na jihar.

Kakakin hukumar, Adamu Shehu ne ya tabbatar da hakan a yau ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

A cewar sa, yaran sun mutu ne a wasu lokuta daban-daban a kananan hukumomin Dutse da Kafin Hausa na jihar.

Shehu ya bayyana wadanda suka rasun kamar haka, Maimuna Hassan ‘yar shekara 3 da ta nutse a ruwa ranar Litinin da kuma Rabi Balarabe ‘yar shekara 12 a ranar Lahadi.

Ya ce, yarinyar ‘yar shekara 3 ta fada cikin ramin magudanan ruwa da ke kauyen Madobi ranar Litinin.

A cewar sa: “Mummunan lamarin ya faru ne a lokacin da yarinyar ta bar gida da misalin karfe 5 na yamma don zuwa wurin ‘yan uwanta su yi wasa a waje, amma ba ta dawo tare da su ba.

“An kaddamar da bincike a unguwar domin gano inda take amma ba a same ta ba, sai da misalin karfe 8:30 na dare.

"Lokacin da wani abokin dan uwanta ya hango rigarta ta dago saman ruwa cikin ramin magudanar ruwan da ke da 'yan mita kadan zuwa gidan su. 

“Sai aka fito da ita daga cikin ruwa, aka garzaya da ita babban asibitin Dutse, amma wani likita ya tabbatar da rasuwar ta."

A halin da ake ciki Balarabe mai shekaru 12 ta nutse a cikin kogi a kauyen Ashuran Makera ranar Lahadi.

Shehu ya ci gaba da cewa: “yarinyar mai suna Rabi Balarabe ta je ta wanke kayanta tare da kawayen ta, bayan ta kammala sai ta yanke shawarar yin wanka wanda abin takaici ya yi sanadiyar mutuwar ta.

“An kai ta babban asibitin Kafin Hausa amma an tabbatar da rasuwar ta, daga baya kuma aka mika ta ga iyayen ta domin yi mata jana’iza."

Hukumar ta kara jajanta wa iyalan mamatan tare da shawartar mutane da su daina barin ramukan magudanan ruwa da ake ginawa a bude. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci