OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

UNICEF Zai Tallafawa Gwamnatin Jigawa Wajen Kawo Karshen Ambaliyar Ruwa

UNICEF Zai Tallafawa Gwamnatin Jigawa Wajen Kawo Karshen Amb

Jihar Jigawa na daga wadanda ambaliyar ruwa ke lalata gidaje, da gonaki tare da rasa rayuka a jihohi Najeriya

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) zai hada gwiwa tare da gwamnatin jihar Jigawa don kawo karshen matsalar ambaliyar ruwa dake addabar jihar.

Jagoran asusun mai kula da ofishinsu na jihar Kano, Rahaman Mahmoud Farah ne ya shaida haka lokacin da tawagarsa ta kaiwa mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ziyarar jajantawa a ofishinsa dake birnin Dutse a karshen makon nan.

Jagoran tawagar yace sun ziyarci ofishin mataimakin gwamnan ne domin jajantawa gwamnati da al`ummar jihar Jigawa bisa asarar rayuka da dukiyoyi da gidaje da kayayyakin amfanin gona sakamakon iftila`in ambaliyar ruwa da afkawa wasu sassa na jihar.

Rahaman Farah ya jaddada bukatar dake akwai ga asusun UNICEF da gwamnatin jihar Jigawa su hada hannu wajen daukar matakan kare ambaliyar ruwa a nan gaba.

A jawabin da ya gabatar mataimakin gwamna, Umar Namadi yayi kira ga asusn UNICEF da sauran hukumomi masu bada tallafi su tallafawa wadanda iftila`in ambaliyar ruwan ta shafa.

Yace ambaliyar ta haddasa asarar rayuka da gidaje da kayayyakin amfanin gona da hanyoyin mota da gadoji da sauran gine-ginen gwamnati da daidaikun mutane a jihar nan.

Mallam Umar Namadi yace gwamnatin jihar Jigawa tana daukar matakan da suka dace wajen killace wadanda ambaliyar ta rushe gidajensu, tare da samar musu abinci da magunguna a sansanin da aka tanadar musu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci