OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jigawa 2023: PDP Ta Kaddamar da Tawagar Kamfen Dauke Da Mutum 27

Jigawa 2023: PDP Ta Kaddamar da Tawagar Kamfen Dauke Da Mutu

Dr Mustapha Sule Lamido

Gabanin zaben gwamna na 2023, jam'iyyar PDP ta jihar Jigawa ta kaddamar da tawagar yakin neman zaben mai adadin mutane 27.

Tawagar kamfen din ta samu halartar dan takarar gwamna na jam’iyyar, Dr Mustapha Sule Lamido a Dutse ranar Litinin.

Lamido ya jaddada bukatar tawagar su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukan su.

Tawagar za ta gudanar da aikin yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam’iyyar a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.

Tawagar za ta kasance karkashin jagorancin Isah Ahmad Duniya Ba Hutu.

A nasa jawabin, Ba Hutu ya yi kira ga ‘yan kungiyar da su hada kai wajen ganin jam’iyyar ta samu nasarar lashe zaben 2023.

Ya kuma yi alkawarin yin aiki bisa ka’idojin jam’iyyar domin samun nasarar jam’iyyar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci