OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojoji Sun Yi Nasarar Tarwatsa Wani Sansanin 'Yan Bindiga Dake Rafin Dawa a Jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta yaba wa kokarin da Sojoji su ka yi wajen fatattakar Sansanin 'yan bindiga dake Rafin dawa a Jihar. 

Sojoji sun kara kaimi a yakin da suke yi da ‘yan bindiga a fadin jihar kaduna, inda suka yi nasarar fatattakar dan bindigar da yayi kaurin suna, Lawal Kwalba da ke zaune a Rafin Dawa wanda ke yankin Dende a karamar hukumar Chikun.

A cewar sanarwar da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce sojojin na Operation Forest Sanity sun gudanar da sintiri zuwa wurin da suka samu bayanan sirri.

“Rundunar sojojin bayan sun gama fatattakan 'yan bindigan sun kwato batura da buhunan taki guda 27.

Wadannan kayan da aka samu sun nuna cewa 'yan bindigan na shirin kera na'urorin fashewa (IED), idan akayi la'akari da kawancen da ke tsakanin yan fashi da 'yan ta'adda.

“Bugu da kari, an samu babur daya da wayoyin hannu guda biyu yayin da ‘yan bindigan suka tsere kafin isowar sojojin.

“Rundunar sojin sun tsawaita bincike a wani wuri dake nesa kadan da sansanin, inda su kayi nasarar kama wasu da ga cikin 'yan bindigan.

Ana ci gaba da bincike kan wadanda ake zargin.

“Gwamnatin jihar Kaduna ta samu rahoton kamen cikin gamsuwa, inda ta yaba da kokarin jami’an da sauran mutanen da ke gudanar da ayyukan,” Mista Aruwan ya kara da cewa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci