OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojoji Sun Ceto Wasu Mutane Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna

Sojoji Sun Ceto Wasu Mutane Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su A

Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun ceto wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun a jihar Kaduna.

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, shine ya shaida wa manema labarai a ranar Talata.

 Aruwan ya ce rundunar sojin ta shaidawa gwamnatin jihar kaduna cewa sojojin su sun yi wa ‘yan ta’addan luguden wuta a lokacin da suke sintiri a kan hanyar Birnin Gwari-Gyam-Kuriga-Manini.

“Sojojin sun yi harbi, inda nan take suka fatattaki ‘yan bindigar, suka gudu zuwa cikin daji suka bar wadanda suka yi garkuwa da su” in ji Aruwan.

Kwamishinan ya bayyana sunayen mutanen da aka ceto kamar haka:Joseph Ishaku; John Bulus; Gloria Shedrack, da 'ya'yanta hudu, Jimre Shedrack; Jonathan Shedrack; Angelina Shedrack da Abigail Shedrack.

“Gwamnatin jihar Kaduna ta yabawa sojojin tare da gode musu bisa jajircewar da suka yi wajen ceto wadanda lamarin ya shafa.

“Mutanen da aka ceto an sada su da iyalan su” in ji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci