OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sanatocin Kudu-Maso-Gabas Sun Roƙi Da a Saki Nnamdi Kanu

Sanatocin Kudu-Maso-Gabas Sun Roƙi Da a Saki Nnamdi Kanu

Gamayyar Sanatoci daga kudu maso gabas na Najeriya sun roƙi gwamnati da ta yi duba akan hukuncin kotu na sakin Nnamdi Kanu.

In za'a iya tunawa a makon da ya gabata ne kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta yi watsi da tuhumar ta’addancin da gwamnati ta yi wa shugaban kungiyar ta IPOB tare da bayar da umarnin sakin shi daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya.

Kotun ta ce matakin ya saɓawa yarjejeniyar miƙa kasar da kuma take haƙƙin Nnamdi Kanu.

An samu cece-kuce bayan da babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ya bayyana cewa kotun ɗaukaka ƙara ta sallami Kanu ne kawai kuma ba ta wanke shi ba.

“Bari a fayyace wa jama’a cewa sauran batutuwan da suka gabata kafin matsalar da ta daɗe tana neman haɗin kan ƙasa da zaman lafiya a tsakanin ƴan Najeriya.

Sai dai wata sanarwa da wasu Sanatoci 14 na Kudu maso Gabas suka sanya wa hannu a ranar Alhamis, ta shawarci gwamnatin tarayya da kada ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin a kotun koli.

"Amma ta buƙaci fadar shugaban ƙasa da ta yi amfani da damar da kotun ɗaukaka ƙara ta bayar tare da la’akari da hanyar siyasa don warware matsalar, cewar Jaridar Punch.

Sanarwar ta samu sa hannun;  Sanata Orji Kalu, Chukwuka Utazi (Mai kare hakkin marasa rinjaye), Enyinnaya Abaribe, Uche Ekwunife, Stella Oduah, Sam Egwu, Obinna Ogba, Theodore Orji, Chimaroke Nnamani, Micheal Nnachi, Onyewuchi Ezenwa, Rochas Okorocha, Frank Ibezim da Ifeanyi Uba  .

Sanatocin sun ce rashin mutunta hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke zai haifar da fassarori daban-daban, wanda ga dukkan alamu illa ce ga haɗin kan ƙasa.

Sanarwar ta ce, “Ya kamata mu yi la’akari da bambance-bambancen mu da kuma irin ƙarfin da mu ke dashi a ƙasa, don kiyaye haɗin kan Najeriya da mutunta bambancinta.

"Saboda haka, mu a matsayinmu na ƴan majalisar wakilai da masu ruwa da tsaki a harkar Nijeriya, muna kira ga shugaban ƙasa, da ya tuna da alƙawarin da ya yi wa tawagar dattawan yankin Igbo a wani lokaci da ya wuce, ya kuma saki Nnamdi Kanu".

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci