OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sakin Nnamdi Kanu, Cewar Lauyan Sa

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sakin Nnamdi Kanu, Cewar Lauyan Sa

Kotun daukaka kara ta umurci gwamnatin Najeriya akan ta saki shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu babban lauyansa, kamar yadda lauya sa, Ifeanyi Ejiofor ya bayyana  a ranar Litinin.

 

A ranar Alhamis ne Kotun daukaka kara da ke Abuja, ta yi fatali da tuhumar taaddanci da gwamnati ta ke yi wa Kanu, tare da bayar da umarnin a sake shi daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

 

An bayyana cewa shugaban na IPOB ya kasance "mai taka doka" ga Najeriya kuma matakin ya sabawa dokar kasa da kuma keta hakkin dan Adam.

 

Sai dai babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis, ta hannun mai magana da yawunsa, Umar Gwandu, ya ce kotun daukaka kara ta sallami Kanu ne kawai amma ba ta wanke shi ba.

​​​​​​

Ya nuna cewa gwamnati ba za ta saki Kanu ba duk da hukuncin da kotu ta yanke.

 

Muna so jamaa su san cewa sauran batutuwan da suka sa muka rike mista Kanu suna nan ba a wanke su ba kuma doka za ta yi dubi da su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci