OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotu Ta Bukaci A Sanar Da Babban Lauya Halin Da Ake Ciki Game Da Lafiyar Abdulrasheed Maina

Kotu Ta Bukaci A Sanar Da Babban Lauya Halin Da Ake Ciki Gam

Abubakar Malami

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin ta umurci mataimakin magatakardan kotun da ya sanar da babban lauyan gwamnatin tarayya, AGF, Abubakar Malami, game da yadda ake ciki akan rashin lafiyar Abdulrasheed Maina.

 

Mai sharia Inyang Ekwo ya ba da wannan umarni ne jim kadan bayan lauyan Maina, Ibrahim Idriss, SAN, ya sanar da cewa ya aiwatar da umarnin kotu na farko kan umurnin da aka bashi akan wanda ake kara a cikin kwanaki uku.

 

Alkalin wanda ya bayar da umarnin ya bayar da sanarwar sauraren karar wanda ake tuhuma.

 

An dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 28 ga watan Oktoba.

 

Maina wanda shine tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho na PRTT, wanda a halin yanzu yake zaman gidan yari na tsawon shekaru takwas a gidan yari na Kuje bisa laifin zamba na kudin fansho kimanin Naira biliyan biyu.

 

A ranar 17 ga watan Oktoba, a cikin korafin da wanda ake tuhuma ya rubuta mai lamba :FHC/ABJ/CS/1729/2022 wanda ya shigar a ranar 27 ga watan Satumba, ya shaida wa kotu cewa yana fama da rashin lafia a gidan yari kuma yana bukatar kulawar gaggawa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci