OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Nnamdi Kanu Ya Shigar Da Kara Kan Cigaba Da Tsare Shi Da Gwamnatin Tarayya Ke Yi

Nnamdi Kanu Ya Shigar Da Kara Kan Cigaba Da Tsare Shi Da Gwa

Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, ya shigar da gwamnatin tarayya kara gaban kotu kan ci gaba da tsare shi da hukumar tsaron farin kaya ta SSS ke yi.

 

A karar da aka shigar a babban kotun tarayya Abuja, Kanu yana neman a gaggauta sakin sa daga hukumar SSS tare da biyansa taran Naira biliyan 100 a matsayin diyya domin tauye hakkinsa na yanci da mutuncin dan Adam da akayi.

 

Kanu ya ce karar da ya shigar ya zama dole ne biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya na yin biyayya ga hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar 13 ga watan Oktoba, inda aka yi watsi da tuhumar taaddancin da ake yi masa.

 

A karar, Kanu ya bayyana cewa ci gaba da tsare shi da gwamnati ke yi daga ranar 13 ga Oktoba zuwa yau, haramun ne, ba bisa kaida ba, zalunci, rashin sanin ya kamata, kuma ba bisa kaida ba.

 

Ya take hakkina na asali na mutunta dan adam, yancin kai da yancin motsi kamar yadda sashe na 34, 35, 36, 39, da 41 na kundin tsarin mulkin 1999 suka tabbatar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci