OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Shugaban Arewa Yayi Tayin Kawo Ƙarshen Kashe-kashe A Yankin Kudu Maso Gabas

Shugaban Arewa Yayi Tayin Kawo Ƙarshen Kashe-kashe A Yankin

Fitaccen shugaban yankin Arewa kuma mai rajin kare hakkin ɗan adam, Alhaji Musa Saidu ya bayyana damuwarsa da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a yankin kudu maso gabas.

Mista Saidu ya yi alkawarin shiga tsakani don kawo karshen kashe-kashen da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suke yi a yankin.

Da yake magana kwanaki kadan bayan harin da aka kai wa Sanata Ifeanyi Uba a jihar Anambra, Alhaji Sa’idu ya bayyana cewa ya taka rawa wajen kawo karshen tashe-tashen hankula a yankin Neja-Delta, inda ya zagaya sansanoni da dama domin kawo ƙarshen rikici tsakanin tsagerun da gwamnatin tarayya.

Alhaji Sa’idu wanda kuma shi ne shugaban Arewa a yankin kudu, ya ce kwanan nan ya samu kira daga wasu mutanen yankim, inda suka bukace shi da ya zo ya kawo zaman lafiya.

“Na yi wata sanarwa a karon baya a cikin takarda, na shawarci shugabannin siyasar Igbo kan matsalar tsaro a gabas, ruwaitowar Jaridar Vanguard.

"Hakan ya biyo bayan kira daga wasu mutanen gabashi da suka ce na shafe sama da shekaru talatin ina samar da zaman lafiya a fadin kasar nan.  

"Suka ce za su so in taimaka wajen kawo zaman lafiya a yankin.  Sun ce an san ‘yan bindigar sosai Kuma suna son in zo in shiga tsakani don dawo da zaman lafiya a  yankin nasu”.

“Sun shirya ganawa tsakanina da wani dan uwan Nnamdi ​​Kanu, Yace Kanu bai shirya raba Najeriya ba. 

"Ya ce wasu ‘yan siyasa sun ci amanar sa, Dukkanmu mun yi wa Muryar Amurka jawabi kan lamarin.

”Na tabbatar musu zan yi iya kokarina Sun ce an san ‘yan bindigar ba ba'a san su ba, Suka ce in jagoranci sasantawar zaman lafiya da suka san ni a matsayin mai gina zaman lafiya sama da shekaru talatin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci