OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sama Da Malamai Goma Aka Kashe A Kaduna —ASUSS

Sama Da Malamai Goma Aka Kashe A Kaduna —ASUSS

Kungiyar malaman makarantun sakandire (ASUSS) reshen jihar Kaduna Najeriya, ta bayyana cewa an kashe malamai sama da 10 a kananan hukumomin Kachia, Chikun, Kagarko, Sanga da Kaura na jihar daga watan Janairun 2022 zuwa yau.

Da yake jawabi a taron manema labarai na bikin ranar malamai ta duniya a Kaduna, shugaban kungiyar ASUSS na jihar, Kwamared Ishaya Dauda, ​​ya bayyana cewa har yanzu sama da malamai 50 ne aka yi garkuwa da su yanzu haka.

Ya bukaci gwamnatin jihar da sauran jami’an tsaro da su tabbatar an sako mambobinsu da daliban da ake tsare da su.

A cewarsa, “Malaman Sakandare sun fi fuskantar matsalar rashin tsaro. Daga watan Janairu zuwa yau, an kashe malamai sama da 10 yayin da ake tsare da sama da 50. An kuma sace wasu daliban.”

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar bisa hadin kan da ‘yan bijilanti suka yi wajen tabbatar da tsaron makarantun inda ya ce, “A kowacce makaranta akwai ‘yan bijilanti akalla shida domin kare malamai da dalibai wanda ke samar da muhalli  mai kyau na koyo.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da ta bullo da tsare-tsare da za su dakile illar hauhawar farashin kayayyaki da kuma tabbatar da biyan ma’aikatan da suka yi ritaya cikin gaggawa domin samun saukin wahalhalun da ma’aikatan jihar ke fuskanta.

Ya kuma tabbatar wa ’yan kungiyar cewa suna aiki tukuru don ganin an aiwatar da sabon shekarun ritaya da aka amince da shi da kuma kyautata jin dadin malaman makarantun sakandare a jihar ta fuskar daukar ma’aikata da karin girma da sauransu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci