OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mazauna garin Birnin-Gwari ta jihar Kaduna sun ce ‘yan ta’addan da aka kashe, sojojin haya ne daga Sudan

Mazauna garin Birnin-Gwari ta jihar Kaduna sun ce ‘yan ta�

Kungiyar Cigaban Masarautar Birnin-Gwari, BEPU, ta bayyana cewa wasu mutane biyu da aka kashe a garin a ranar lahadi 'yan ta'addan haya ne daga kasar Sudan.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta yi Allah wadai da kisan wasu makiyaya biyu da wasu ’yan daba suka yi a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata.

Sakon yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya fitar.

Ya ce jami’an tsaro sun bayar da rahoton cewa ’yan daban sun kwace makiyayan biyu ta karfi a hannun jami’an tsaro bisa zargin cewa suna da alaka da ‘yan ta'adda.

Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar mazauna yankin Ishaq Kasai ya fitar ya ce gwamnatin jihar ta yi gaggawar fitar da sanarwa da ba gaskiya ba, ba tare da bincikar sunayen wadanda aka kashe ba.

 “BEPU, wata kungiya ce mai zaman kanta domin habaka zaman lafiya inda a fili take adawa da duk wani nau’i na ’yan daba a karkashin ko wane irin tsari kuma tana jan hankalin ‘yan kasa da kada su dauki doka a hannunsu duk da irin bacin rai da suke ciki.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci