OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

El-Rufa'i ya mayar da martani game da kashe wasu makiyaya da aka yi a Kaduna

El-Rufa'i ya mayar da martani game da kashe wasu makiyaya da

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya yi Allah-wadai da kisan wasu makiyaya da wasu gungun mutane suka yi.

An kwace makiyayan ne a hannun jami’an tsaro a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar.

Rahotanni sun ce an zargi makiyayan da alaka da ‘yan bindiga. 

Majiyoyi sun bayyana cewa gungun mutanen sun kwace mutum biyun ne daga hannun jami’an tsaro tare da kona su.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi.

Aruwan ya ce gwamnan ya yi bakin ciki da wannan aika-aikar .

A cewar sanarwar: “Gwamna El-Rufa’i ya nuna matukar damuwar sa kan aika-aikan da gungun mutanen suka aikata, ya kuma yi Allah wadai da kashe makiyayan ba bisa ka’ida ba.

"Ya sake bayyana muhimmancin bin hanyoyin da suka dace a matsayin zabin da aka amince da shi kawai wajen fuskantar duk wani tuhuma na aikata laifuka."

Gwamnan ya kara da yin kira da a kwantar da hankula daga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su yayin da yake bada odan gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci