OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kashe Kasungumin Dan Ta'addan Nan Uzaifa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kashe Kasungumin Dan Ta'addan Nan

A jerin gwanon harin da Rundunar sojin ke kaiwa Yan ta'adda tayi nasarar kawo karshen Shugaban kungiyar ISWAP dake jagorantar Yan ta'addan sambisa mai suna Uzaifa.

Uzaifa me rike da mukamin Minzir ma'ana na hudu a jerin masu jiran gadon shugabancin kungiyar ISWAP baki daya ya karbi ragamar jagorancin sansanin yan ta'addan na dajin sambisa bayan mutuwar Abubakar Shekau.

Yayin wani sumamen hadin gwiwa tsakanin Rundunar sojin sama da na kasa Uzaifa tare da yaransa 37 sun rasa rayukansu.

Darektan yada labarai na rundunar manjo janar Musa Dan madami ne ya tabbatar da faruwar hakan a yau Alhamis yayin taron manema Labaran da aka gabatar a birnin tarayya Abuja.

Ya kuma Kara da cewa a yunkurin rundunar na kawo karshen ta'addanci a yankin Arewa maso gabashin Kasarnan sunyi nasarar dakile wasu sansanin yan ta'addan dake jihohin Niger, Plateau, Kaduna da Abuja.

Manjo janar Danmadami ya kuma bayyana cewar rundunar tayi nasarar kama Naziru Muhammad wanda yake saidawa Yan ta'addan bindigu sun kuma kwace muggan makamai hadi da harsashi guda 1000 a mafakarshi dake jihar Kogi yayin wani sumamen da suka kai.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci