OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rundunar sojin Najeriya ta karrama sojoji masu hazaka da ke yaki da Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta karrama sojoji masu hazaka da ke

Nigerian Army decorates officers, journalists in counter insurgency war

Mukaddashin kwamandan sashi na uku na Operation Lafiya Dole da rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa, birgediya Abdulsalam Abubakar, yayi wa sojoji ado bisa jajircewar su wajen yaki da 'yan ta'adda.

Abubakar yace al'ada ce a gidan soja a girmama wadanda suka cancanta yayin da suka bambanta kan su wajen aiki. 

Ya kuma bukace su da su ci gaba da kara himma wajen yi wa kasa hidima, inda ya kara da cewa bikin karramawar ya kasance alama ce da ta zo daidai da cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yancin kai.

A yayin da yake tunatar da sojoji dubunnan kalubalen tsaro da suka addabi al'ummar kasar nan, da kuma yanayin tattalin arzikin ta, ya umarci dukkan sojojin da su kasance masu tsayin daka, da juriya da kwarewa don shawo kan dukkan kalubalen.

Kwamandan ya mika godiyarsa ga babban hafsan tsaron kasar Leo Irabor da babban hafsan sojin kasa Faruk Yahaya bisa goyon bayan da suke baiwa sojojin wanda a cewar sa har yanzu abu ne mai kara kuzari.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci