OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jami’an NIMC Na Jabu Sun Bude Ofis A sansanin ‘Yan Gudun Hijirar Jamhuriyyar Nijar

Jami’an NIMC Na Jabu Sun Bude Ofis A sansanin ‘Yan Gudun

Jami’an tsaro da suka hada da sojojin Najeriya da na hukumar shige da fice da kuma ‘yan sandan Najeriya sun cafke wasu jami’an jabu guda biyu na hukumar da ke sa ido kan bayanan sirri na NIMC a Jamhuriyar Nijar.

 Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na rundunar sojin Manjo Janar Musa Danmadami, ya bayyana hakan ga labarai a wani taron manema labarai a hedikwatar tsaro da ke Abuja a yau Alhamis.

 Dan madami ya zayyana kayayyakin da jami’an tsaro suka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da: Na’urar rajista ta kasa (NIN), na’urar buga takarda, injin laminating, na’urar bin diddigin kwamfuta da injin janareta da dai sauransu.

 Danmadami ya bayyana "A ranar 13 ga Oktoba, 2022, sojoji tare da ‘yan sandan Najeriya da jami’an NIS sun kama wasu mutane 2 da ake zargin jami’an hukumar kula da shaidar dan kasa (NIMC) na bogi me"

 Da yake tsokaci game da ci gaban yayin gabatar da tambayoyi daga manema labarai, babban darekta na DMO, Manjo Janar Benard Onyeuko, ya ce za a warware aniyar wadancan jami’an jabun.

 Ya ce wannan babban nasara ce ga jami'an sojin kuma ya kamata a yaba musu.

 Wadanda ake zargin, a cewar rundunar sojin kasar, an kama su ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Gagamari a jamhuriyar Nijar a lokacin da suke yi wa wadanda ba ‘yan Najeriya rijista ba tare da sanya su a asusun ajiyar bayanan Najeriya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci