OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 11 Watanni da suka shude

Sojojin Najeriya sun fatattaki mayakan Boko Haram a Borno

Sojojin Najeriya sun fatattaki mayakan Boko Haram a Borno

Sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun dakile wani hari da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai a jihar Borno.

‘Yan ta’addan sun yi wa sojojin kwanton bauna ne a lokacin da suke rakiyar motocin fasinja a kan hanyar Damboa.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, wani kwararre kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce sojojin sun fatattaki ‘yan ta’addan ne yayin da mutanen da ke cikin motocin suka nemi tsira da rayukan su.

A cewar sa: "'Yan jihadin sun yi ruwan wuta mai tsanani kan ayarin motocin sojojin da ke tafiya a cikin motoci masu sulke da taushi, tare da rakiyar motocin fasinja amma a halin yanzu sojojin na mayar musu da martani."

Ya kara da cewa "Har yanzu babu takamaiman adadin wadanda suka rasa rayukan su."

Idan dai za a iya tunawa dai kwararren kan harkokin tsaro ya bayyana shirin da ‘yan ta’addan suka yi wa wasu sojoji kwanton bauna a yankin Arewa maso Gabas.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai