OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kona Jirgin Da Aka Sace Danyen Man Fetur Ya Saba Wa Doka- Falana

Kona Jirgin Da Aka Sace Danyen Man Fetur Ya Saba Wa Doka- Fa

Femi Falana

Lauyan kare hakkin bil Adama, Mista Femi Falana, SAN, a jiya, ya yi zargin kona wani jirgin danyen mai da sojoji suka yi, inda ya bayyana shi a matsayin laifi.

 

 A makon da ya gabata ne wata tawagar jami'an tsaro da Ke sa Ido kan bututu mai zaman kanta Tantita security service ta kama wani jirgin ruwa dauke da danyen man fetur da aka sace, daga bisani kuma jami'an sojin yankin suka banka ma Jirgin wuta. 

 

 Sai dai da yake tsokaci kan lamarin Femi Falana, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce:

“Abin kunya ne yanda babban hafsan sojin kasa, Janar Lucky Irabor ya ce gaggawar lalata jirgin ruwan da ake zargin masu laifin sun sato mai akai ya yi daidai da ka'idojin aiki"

"Janar Lucky ya mara was jami'an sa baya tare da tabbatar da cewa bankawa jirgin wuta ba tare da gabatar da wani bincike ba daidai ne domin an same shi dauke da danyen Man da aka sato".

Saide Falana ya ce bisa tanadin doka babbar kotun tarayya ce kadai ke da ikon ba da umarnin kwace wani jirgin ruwa da aka yi amfani da shi wajen jigilar danyen mai da aka sace.

Bisa wannan dalilin, lauyan ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari, yayi gaggawar korar sa.

"Sannan kuma ya kamata shugaban kasa ya umarci babban hafsan sojin kasar da ya tabbatar da kamo jami’an sojin da suka kona jirgin da nufin gurfanar da su da laifin kone-kone a gaban kotun soji.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci