OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rikicin Jam'iyya: PDP Ta Yi Kasa A Gwiwa - Keyamo

Rikicin Jam'iyya: PDP Ta Yi Kasa A Gwiwa - Keyamo

Karamin Ministan Kwadago Festus Keyamo ya yiwa jam'iyyar PDP ba'a kan rikicin da ya dabaibaye ta.

 Keyamo ya ce jam’iyyar ta rasa yadda za ta yi amma kullum tana zuwa ta ce tana son ceto Najeriya.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya yi wa PDP kaca-kaca da yammacin Laraba a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

 Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sansanin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a ranar Laraba ya fice daga majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP, inda suka dage cewa sai shugaban jam'iyyar na kasa Iyorchia Ayu ya yi murabus kafin su shiga yakin neman zabe.

 A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Keyamo ya ce, “Jam’iyyar PDP da ke cikin rikici saboda gazawarta wajen sarrafa laimarta dada karuwar kullum Amman da zarar sun Bude baki sai kaji sunce suna son ‘ceto’ Najeriya ne; kamar matashin da kafafuwansa suka kasa tabo accelerator mota yace yana son tuka tirela"

 Rikicin PDP ya ci gaba da ruruwa yayin da kiran murabus din Ayu ya ci gaba da haifar da cece-kuce. Wike da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne suka jagoranci wannan kiran, inda Atiku ya jaddada cewa ba za a tilastawa Ayu yin murabus ba.

Atiku a ranar Laraba, ya ce, “Game da kiraye-kirayen yin murabus ko tsige shugabanmu na kasa, duk da haka, dole ne in sake maimaita abin da na fada a fili da kuma a boye; hukuncin Dr. Iyorchia Ayu na yin murabus daga mukamin na shi ne shi kadai, ni ko wani ba mu da hurumin da zamu iya tursasa masa”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci