OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Peter Obi Ya Nemi Afuwa, Yayi Alƙawarin Gyara Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa

Peter Obi Ya Nemi Afuwa, Yayi Alƙawarin Gyara Kwamitin Yaƙ

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi a ranar Juma'a ya nemi gafarar magoya bayansa kan jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar.

Obi wanda ya yi wannan roƙo ne ta shafin sa na Twitter inda ya tabbatar da cewa za a sake duba jerin sunayen da ake ta cece-kuce.

Obi yace, “Na sami ƙiraye-ƙirayen damuwa da yawa bayan fitar da jerin sunayen kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugabancin Jam’iyyar Labour.  

"Tabbas, akwai wasu kurakurai da aka shigar a ciki, don haka masoya na suka bayyana damuwar su."

A martanin da shugaban jam’iyyar Labour yayi a wani taron manema labarai yace zasu yi gyara akan wannan matsala nan kusa.

"Dangane da alƙawarin mu na yin adalci da gaskiya, za a fitar da sabbin jerin sunaye a kan lokaci, Ina roƙon a yi haƙuri.”

Jam’iyyar ta gabatar da jerin sunayen mambobi 1,234 na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a 2023 a wani taron da aka gudanar a ranar Laraba a Abuja.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa daga cikin waɗanda aka lissafa akwai Manjo Janar na Sojojin Najeriya mai ritaya, John Enenche.

An kuma yi kuskuren saka sunayen shugabannin ƙungiyar kwadago ta Najeriya da kuma mambobin ƙungiyar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci