OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

PDP: wata kungiya ta bukaci Atiku ya sa baki Ayu ya yi murabus

PDP: wata kungiya ta bukaci Atiku ya sa baki Ayu ya yi murab

Wata kungiya mai suna Alliance for Social Justice in Nigeria, ta bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, da ya yi magana akan Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga mukaminsa domin samun kwanciyar hankali a jam'iyyar.

Matsayar kungiyar na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fitar bayan wani taro daya gudana a ranar Asabar a garin Abuja.

Kungiyar ta bayyana fargabar cewa rikicin shugabancin jam’iyyar zai iya ragewa jam’iyyar karfi wanda ka iya lalata dimokuradiyyar Najeriya.

“Tsayayyiyar Jam’iyyar adawa ita ce ginshiki na dorewar dimokaradiyya ta gaskiya, don haka rikicin PDP ka iya sawa jam’iyyar APC mai mulki ta yi mata zarra ga ci gaban dimokuradiyyar Najeriya,” in ji kungiyar.

Sanarwar ta samu sa hannun shugaban kungiyar, Sylvanus Ukpong; Mataimakin sa, Aliyu Oboshi; Sakatare Janar, Aniche Paulina; da mai magana da yawun kungiyar, Jesse Bello.

“Son kai shi ne ya ta'azzara rikicin PDP saboda shugabannin jam’iyyar ba su yi tunani ba tunda suka jefe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar zuwa dukkan shiyyoyin Najeriya maimakon a mayar da shi yankin Kudu tun da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito daga yankin Arewa.

“Mun yi imani da cewa samun shugaban kasa daga yankin Kudu a 2023 zai iya taimakawa wajen rage kabilanci da kuma inganta hadin kan kasarmu mai daraja.

“Tunda jam’iyyar PDP ta riga ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takararta na shugaban kasa, muna ganin ba komai ba ne dan mun bukaci Sanata Iyorchia Ayu ya sauka daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Idan Ayu ya sauka yankin Kudu zai daidaita za a kuma samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jam’iyya kafin zaben 2023, "in ji kungiyar a cikin sanarwar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci