OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

NYSC: Dalibai Hudu Za Su Maimaita Hidimar Kasa

NYSC: Dalibai Hudu Za Su Maimaita Hidimar Kasa

Hukumar kula da​​​​​​ yiwa kasa hidima ta NYSC reshen jihar Bauchi, a yau Alhamis ta bayyana cewa mutane hudu na Batch C stream 1 na shekarar 2022, za su maimaita shekarar hidimar su a jihar.

Namadi Abubakar, Kodinetan hukumar a jihar je ya bayyana haka, inda yace za a kara wa wasu mutum 27 shekarar hidima na makonni uku saboda munanan dabi'u da suka nuna lokacin da suke bakin aiki. 

Abubakar ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Bauchi a lokacin karbar takardar shaidar kammala aikin da ‘yan bautar kasa ke yi.

Ya ce an hukunta wadanda abin ya shafa saboda laifuka daban-daban da suka hada da tserewa da kuma rashin zuwa a lokacin aikinsu.

Mista Abubakar, ya nanata cewa hukumar ba za ta dauki rashin zuwa aiki ba kuma ba za ta yi shakkar hukunta duk wanda ya yi ba daidai ba.

A cewarsa, daga cikin ’yan bautar 1,151 da aka ya ye, biyar daga cikinsu za a karrama su da lambar yabo ta jiha bisa gagarumin gudunmawar da suka bayar wajen inganta rayuwar al’ummar da suka karbi bakuncinsu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci