OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane 11 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Bauchi

Mutane 11 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Bauchi

Wani hatsarin mota da ya afku a jihar Bauchi, ya halaka mutane 11 yayin da wasu da dama suka jikkata a ranar Asabar.

Hatsarin ya afku ne a ƙauyen Hawan Jaki dake kan titin Alƙaleri zuwa Gombe a ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.

Kwamandan sashi na hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) dake jihar Bauchi ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

Ya ƙara da cewa wasu mutane takwas sun samu munanan raunuka a haɗarin.

Kwamandan sashin ya ƙara da cewa hatsarin ya haɗa da motar fasinja guda daya na mkmafanin Yankari Express da kuma wata mota ta Dangote.

Abdullahi ya alaƙanta musabbabin hatsarin da tuki mai hatsarin gaske.

“Maza 20 ne mummunan hatsarin ya rutsa dasu.

“Tara daga cikinsu sun rasa rayukansu nan take yayin da biyu kuma jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu a babban asibitin Alƙaleri.

“Wasu takwas kuma sun samu raunuka daban-daban kuma suna karbar magani a asibitin Alƙaleri inda aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu,” inji shi.

Abdullahi ya shawarci masu ababen hawa da su rika kiyaye ka’idojin ababen hawa a kodayaushe yayin da suke tafiya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci