OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnan Bauchi ya 'yanta fursunoni 153, ya baiwa kowannen su N50,000

Gwamnan Bauchi ya 'yanta fursunoni 153, ya baiwa kowannen su

Governor Bala Muhammad of Bauchi state

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya 'yanta fursunoni 153 da ke zaman gidan yari akan kananan laifuka daban-daban. 

A matsayin tallafi, gwamnan ya baiwa fursunonin jarin N50,000 kowannen su domin su fara kasuwanci. 

Da yake jawabi a wajen bikin sakin nasu, gwamnan ya ce tallafa wa fursunonin zai kasance mai amfani ga kowa.

A cewar sa: “Mutanen da zan yi wa afuwa a yau, ba su da wani amfani ga al’ummar su idan aka bar su suna cikin wahala tare da masu taurin kai.

"Zan yi musu afuwa tare da fatan za su koma su zama abin dogaro ga al'ummar su, su kuma yi aiki don tallafa wa iyalan su, jihar mu da al'ummar mu abin kauna."

“Muna baiwa kowane fursunan da aka ‘yanta kudi naira 50,000 domin fara kananan sana’a da nufin dogaro da kai."

Gwamnan ya kara da cewa "Mun yi imanin cewa karfafa wa talakawa ta karfin tattalin arziki na daya daga cikin mafi kyawun hanyoyin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kuma rigakafin aikata laifuka."

Ya kuma bayyana cewa ya biya jimillar Naira miliyan 1.2 na tarar da kotu ta ci fursunonin. 

Ya bayyana cewa ya biya kudin ne daga aljihun sa. 

Babbar mai shari’a a jihar, Rabi Talatu Umar ta ce matakin da gwamnan ya dauka zai taimaka wajen rage cunkoso a gidajen gyaran hali na jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci