OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zulum fitilla ne cikin gwamnoni, cewar Gwamnan Bauchi

Zulum fitilla ne cikin gwamnoni, cewar Gwamnan Bauchi

Governor Babagana Umara Zulum

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kasance fitila cikin gwamnonin Najeriya da dabarun jagoranci.

Mohammed wanda gwamna ne karkashin jam’iyyar PDP ya bayyana hakan a Bauchi ranar Lahadi, a lokacin da Zulum ya kai masa ziyarar ta’aziyyar rasuwar dan uwan sa, Bappa Mohammed.

A cewar gwamnan, salon shugabancin Zulum ya kawo daukaka ga al’ummar Arewa maso Gabas da ma kasa baki daya.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, gwamnan yace: “Farfesa Zulum, ka zana wa kanka wani katafaren suna a matsayin shugaban da ke ba mu haske a kasar nan.

“Ka yi abubuwa da yawa kuma ba shakka salon shugabancin ka ya cancanci a kwaikwaya.

“Shugabancin ka ya kawo alfahari ga daukacin mu a wannan yanki na kasar nan a Arewa maso Gabas. 

"Ka jajirce duk miyagu da suke kai mana boma bomai, ’yan ta’addan Boko Haram sun watse.

“A yau, ko shugaban kasa yana da alfaharin kasancewa tare da kai. 

"Kai ne Gwamnan da shugaban kasa ya fi ziyarta kuma wannan a zahiri yake."

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci