OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane Fiye da 200 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC A Jihar Delta

Mutane Fiye da 200 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC A Jiha

APC/PDP

Ɗaya daga cikin jiga-jigan jam'iyar PDP a jihar Delta, Prince Gabriel Nwanazia, ya koma jam’iyyar APC tare da sama da mutane 200.

Nwanazia wanda ya koma APC a ranar Asabar a karamar hukumar Aniocha ta Arewa tare da magoya bayansa ya ce ya koma APC ne sakamakon rigingimun da ba a warware ba a PDP.

"Ni ƙwararre ne mai wayar da kan jama’a na PDP, babban mataimaki amma a yau na yanke shawarar ni da magoya bayana sama da dari biyu zuwa APC.

“PDP ba ta cika alƙawari, na yi wa PDP aiki tsawon shekaru, na yi wa PDP hidima a duk zaɓukan da aka yi a Aniocha ta Arewa.

“A yau babu wani ci gaba a yankinmu, wasu abubuwa a nan APC ce ta yi, gashi jam'iyar na fama da rikici ko’ina"

Da yake gabatar da waɗanda suka sauya sheƙan ga shugabannin jam’iyyar, kansilan jam’iyyar APC daya tilo a jihar Delta, Mista Emmanuel Oweazim, ya bayyana cewa Nwanazia ne matsalar APC a ƙananan hukumomi a lokutan zabe a baya.

“2023 ita ce ƙarshen PDP a jihar Delta, ɗaya daga cikin matsalolinmu lokacin zaɓe ya koma APC a yau kuma ana sa ran mutane da yawa za su koma APC nan ba da jimawa ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Rikicin ya sa PDP ta rasa ɗaya daga cikin jiga-jigan ta kuma in Omo-Agege ya zama gwamna a 2023, ba zan zama kansila ɗaya tilo a jihar ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci