OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

MURIC Ta Buƙaci Majalisar Dokoki Ta Sanya Dokar Hukunta Shigar Rashin Tarbiyya

MURIC Ta Buƙaci Majalisar Dokoki Ta Sanya Dokar Hukunta Shi

Ƙungiyar nan dake rajin haƙƙin ɗan Adam ta Musulunci wato MURIC, ta buƙaci Majalisar Dokoki ta ƙasa da ta kafa dokar da za ta haramta sanya tufafin da bai dace ba a Najeriya.

Daraktan hukumar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi wannan roƙo a wata sanarwa ga manema labarai a ranar Alhamis.

Ishaq yace ya kamata ƴan majalisar su sake duba sashe na 26 na dokar hana cin zarafin jama’a na shekarar 2015.

Daily Nigerian ta ruwaito daraktan na cewa kungiyar ta yi tir da na cin zarafin mata da maza, inda ya koka da cewa maza na fama da cin zarafi daga mata.

Yayi kira da a yi gyara ga dokokin ƙasar kan cin zarafi, ya ce bai kamata a nuna fifiko ga mata ba, ya ƙara da cewa mata suna da laifi kamar maza koma su fisu.

“Bai kamata a nuna wa mata fifiko a kan abin da ya shafi lalata da su ba, Mata suna da laifi kamar maza idan har basu fisu ba.

"Fyade yana ƙaruwa a cikin al'umma a yau saboda lalacewar dabi'a da ta kai ƙololuwa.

 “Yanzu mata na buɗe sassan jikinsu don su tada hankali a bainar jama’a, Munason a samu  dokar ƙasa don kula da hakan.”

Akintola ya yi kira ga majami’u da masallatai da su yi yaƙi da sanya tufafin da bai dace ba, yana mai cewa addinan biyu sun yi tir da wannan aika-aika.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci