OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamna Adeleke ya bukaci gwamnatin Afrika ta kudu ta dakatar da cin zarafin da akewa Yan Najeriya

Gwamna Adeleke ya bukaci gwamnatin Afrika ta kudu ta dakatar

Gwamna Ademola Adeleke ya roki mahukuntan kasar Afirka ta Kudu da su sa baki tare da dakatar da cin zarafi da cin mutuncin ‘yan Najeriya da ake yi a Afirka ta Kudu. 

 

Gwamnan yayi wannan kira a lokacin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Afirka ta Kudu a Najeriya, Farfesa Bobby J Moroe, da mataimakinsa, Ms Busisiwe Dlamini a gidan gwamnati.

 

Gwamnan ya bayyana kiyayyar ake nunawa 'yan Najeriya mazauna Afrika ta kudu a matsayin abin damuwa matuka dake barazana ga kyakyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

 

 "Ina rokon ku da ku isar da damuwarmu ga gwamnatin ku. Ba daidai ba ne ayiwa al'ummar kasar baki ɗaya kudin goro a matsayin masu laifi. Kowace kasa tana da alumma masu gaskiya da marassa gaskiya. A Afirka ta Kudu, akwai dubban ‘yan Najeriya da ke gudanar da harkokinsu na kasuwanci da ayyukansu. Suna shan bakar wahala saboda mummunar fahimtar da akayi musu" a cewar Adeleke 

 

 "Muna bukatar mu kawo karshen wannan cin zarafi da ake yi wa ‘yan kasarmu a kasarku" ya jaddada.

 

A nasa jawabin jakadan ya bayyana cewa sunji damuwar da mai masaukin bakin ya gabatar amma ya kara da cewa gwamnatinsa na yin kokari matuka wajen ganin an samar da fahimtar juna tsakanin yan kasar da Yan Najeriya domin kawo karshen cin zarafin da suke fuskanta.

 

A cewarsa "Gwamnatin Afirka ta Kudu na mutunta dangantakarta da Najeriya idan aka yi la'akari da dumbin tarihin 'yan uwantakar mu da kuma kusancin tattalin arziki da diflomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu. Zamu isar da damuwar daka bayyana ga shugaban kasar mu"

 

Gwamna Adeleke da jakadan Afrika ta kudun sun yi nazari kan damarar tattalin arzikin da ke tsakanin kasashen biyu, tare da gabatar da wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin jihar Osun da lardin Gauteng na Afirka ta Kudu, wanda shi ne mafi ci gaban lardunan Afirka ta Kudu. 

 

Bangarorin biyu sun amince suyi musayar fasahohin sarrafa kayan gona da hakar ma'adinai.

 

Yankin Gauteng yana ba da gudummawar kashi 33.9% ga yawan kudin shigar cikin gida na Afirka ta Kudu (GDP) kuma yana ɗaya daga cikin manyan masu ba da gudummawa ga tattalin arzikin nahiyar. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci