OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Muna sane da inda wadannan ‘yan bindigan suke – El-Rufa’i

Muna sane da inda wadannan ‘yan bindigan suke – El-Rufa�

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i| Hoto Daga: BBC

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa gwamnati ta san inda 'yan bindigan da suka addabi yankin arewa maso yamma suke.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock a Abuja.

Ya ce akwai taswirorin da ke nuni da inda 'yan bindigan suke amma sai an shirya kafin a tinkare su.

"Eh, mun san inda wadannan 'yan fashin suke, muna da taswirori. Amma sai wani ya shiga ya kashe su. Ni bazan iya yin haka ba. Idan wanin bai da isassun mayaka, ba shi da isasshen kayan yaki, ba shi da fasaha, babu wanda zai je ya kashe kansa," in ji El-Rufa'i.

Ya kuma bayyana cewa hadin gwiwar gwamnatin tarayya da kungiyar gwamnonin Najeriya ne suka jawo mallakar jiragen Super Tucano da sojoji ke amfani da su.

Ya kara da cewa an dauki matakin ne domin karfafa tsarin tsaron kasar.

Gwamnan ya kuma yi kira da a rika kai hare-hare ta kasa da sama a lokaci guda domin ganin ‘yan ta’adda sun ji karfin sojojin Najeriya tare da samun sakamako mai inganci.

Yayin da ya ce hare-haren a lokaci guda na iya haifar da asarar rayuka da ba su ji ba ba su gani ba, ya kuma kara da cewa gwamnatin sa a shirye take ta yi kasadar tabbatar da jihar Kaduna cikin kwanciyar hankali.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci