OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mazauna Bauchi Sun Yi Farin Ciki Da Komawa Aikin Jirgin Kasa Na Cikin Gari

Mazauna Bauchi Sun Yi Farin Ciki Da Komawa Aikin Jirgin Kasa

Photo Source: The Cable

Al’ummar jihar Bauchi sun bayyana jin dadin su kan yadda aka dawo da zirga-zirgar jirgin kasa a cikin jihar.

Mazauna yankin da suka bayyana jin dadin su ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), sun yaba wa kamfanin jiragen kasa na Najeriya (NRC) bisa farfado da ayyukan jirgin kasan. 

Hukumar NRC ta gyara layin dogon na kilomita biyar daga babban birnin jihar zuwa wata gari da ke kan hanyar Bauchi zuwa Gombe.

A cewar mazauna yankin, farfado da sufurin jiragen kasa zai inganta zamantakewa da tattalin arziki a jihar.

Wani mazaunin garin mai suna Mista Michael Habu ya bayyana jin dadin sa, inda ya ce: “Da dawo da aikin jirgin kasa, zan tafi Bauchi ta jirgin kasa domin yin aiki na."

Wani mazaunin garin, Mudi Sagir cike da farinciki ya ce aikin zai zama abin bude ido ga yaran da basu san irin wannan tsarin sufurin ba.

A cewar sa: “Sake dawo da ayyukan jirgin kasa na daya daga cikin abubuwan da suka faru ga al’ummar wannan yanki.

"Kuna iya ganin farin ciki a fuskokin su, duk mun yi farin ciki da abin da ke faruwa. Mai yiwuwa ya dore bisa la'akari da muhimmancin sa ga al'umma."

Haka kuma manajan kamfanin jirgin, Mista Aliyu Mainasara ya ce jirgin na da kujeru 100 kana da jami’an tsaro don ba da kariya ga mutane.

Da yake mayar da martani kan farashin kudin jirgin, ya ce kowane fasinja zai rika biyan Naira 200 na tafiya guda. 

Ku tuna cewa Hukumar NRC ta dakatar da aiyukan jiragen kasa a cikin shekaru 10 da suka gabata a jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci