OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Matsalar Tsaro Zai Zo Karshe a Watan Disamba, cewar Ministan Cikin Gida

Matsalar Tsaro Zai Zo Karshe a Watan Disamba, cewar Ministan

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa za a kawo karshen tabarbarewar tsaro a kasar nan da watan Disamba.

Mista Aregbesola ya ba da wannan tabbacin ne lokacin da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta yi hira da shi a Abuja.

Ministan ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa jami’an tsaro wa’adin watan Disamba domin su dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan sassan kasar nan.

Ya ambato abinda shugaba Buhari ya bayyana inda ya ke cewa ba zai bar kasar nan ba tare da ya magance matsalolin tsaro yadda ya kamata ba.

“Ya ba da wa’adin kawar da barazanar rashin tsaro na rayuka da dukiyoyi kafin watan Disamba.

“Na yi imanin cewa babu wanda ya nade hannunsa ba tare da taya gwamnati ta wanzar da doka da oda ba , da kuma tabbatar da tsaro.

“Muna akan manufar mu, dole ne mu tambayi kanmu, cewa mulki shine tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

“Za mu kawar da duk matsalolin rashin tsaro nan da Disamba.

"Idan ka dubi yadda al'amura ke gudana a Najeriya, za kaga cewa an samu ci gaba da dama a cikin shekarun nan," in ji shi.

Mista Aregbesola ya bayyana cewa kafin shekarar 2015 ‘yan Najeriya na fama da bama-bamai a ko’ina.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci