OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Majalisar zartarwar APC ta Kano tayi watsi da dakatar da Ganduje

Majalisar zartarwar APC ta Kano tayi watsi da dakatar da Gan

Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano State

Majalisar zartarwar jam’iyyar APC ta jihar Kano tayi watsi da dakatar da shugaban jamiyyar Abdullahi Umar Ganduje da shugabannin mazabar Ganduje sukayi

 

 Abdullahi Abbas, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin. 

 

A cewarsa, an dakatar da shugabannin mazabar Ganduje na tsawon watanni shida saboda cin dunduniyar jamiyyar da suka aikata.

 

Abbas ya bayyana cewa kwamitin zartarwar jamiyyar na Jihar be amince da matakin dakatarwar ba saboda haka "kwamitin ya amince da sanya musu takunkumi na tsawon watanni shida, kuma an dakatar da su." Shugaban jamiyyar ya jaddada.

 

A ranar Litinin ne kwamitin zartarwar mazabar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa suka sanar da dakatar da Dakta Ganduje bisa zargin cin hanci da rashawa.

 

Haladu Gwanjo, mashawarcin jamiyyar APC a mazabar ya ce sun yanke shawarar dakatar da Ganduje sakamakon girman zarge-zargen cin hanci da rashawa, musamman faifan bidiyon dala da aka yi ta yadawa. Sai dai, Kwamitin zartarwar jamiyyar na Jihar ya ce dakatarwar ba ta da tushe, don haka ba za ayi aiki da ita ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci