OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mafi Karancin Albashi: NLC Ta Bada Wa'adin Kwanaki 21 Ga Gwamnatin Zamfara

Mafi Karancin Albashi: NLC Ta Bada Wa'adin Kwanaki 21 Ga Gwa

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) reshen jihar Zamfara ta bayar da wa'adin kwanaki 21 ga gwamnatin jihar kan aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000.

Shugaban kungiyar NLC na jihar Sani Haliru ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Gusau.

Haliru ya ce majalisar zartaswar kungiyar ta jiha ce ta dauki matakin a taron ta.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, Haliru ya ce: “Mun gama da duk wata hanyar tattaunawa da gwamnati, yanzu ya rage mana mu shiga yajin aikin domin ganin an ba mu hakkin mu."

Ya kuma yi watsi da rahotannin kafafen sada zumunta na cewa gwamnatin jihar na biyan kashi 70 na mafi karancin albashi.

Ya kara da cewa gwamnan jihar Bello Matawalle ya yi alkawarin fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 a watan Yuni amma ba a cimma ruwa ba.

Shugaban ma’aikata a jihar ya yi alkawarin cewa za a fara biyan a watan Agusta amma ba'a cika alkawarin ba, ya kara da cewa.

A cewar sa: “Ba za mu iya ci gaba da nade hannayenmu mu kyale gwamnatin jihar ta dagula ma’aikata a jihar ba."

Ya jaddada cewa bayan wa’adin kwanaki 21, kungiyar za ta tsunduma yajin aiki har sai an biya bukatar su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci