OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotu Ta Wanke Jonah Jang Daga Zargin Almundahanar N6.3bn

Kotu Ta Wanke Jonah Jang Daga Zargin Almundahanar N6.3bn

Jonah Jang leaving court after being discharged

Wata babbar kotun jihar Filato, a ranar Litinin da ta gabata a Jos, ta sallami Sanata Jonah Jang da Yusuf Pam daga zargin cin hanci da rashawa na Naira biliyan 6.3 da Hukumar Hana yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Jonah Jang, tsohon gwamnan Filato da Mista Yusuf Pam, wanda tsohon kashiya a ofishin sakataren Gwamnatin jihar a gaban kotu kan tuhume-tuhume 17 da suka shafi karkatar da kudaden jihar tun ranar 4 ga watan Mayun shekarar 2018.

Alkalin kotun, Mai shari’a Christen Dabup, wanda ya yanke hukuncin, ta ce kotun ba ta samu Jang da Pam da wani laifi ba.

“Kotu ba ta sami wadanda ake tuhumar da laifin ko daya daga cikin tuhume-tuhumen ba kuma an sallame su an kuma wankesu daga dukkan wani zargi” in ji ta.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Cif Mike Ozekhome (SAN), Lauyan da ke kare wadanda ake tuhuma, ya ce kotun ba ta same su da laifin komi ba a cikin tuhume-tuhume 17 da ake tuhumar su da su.

Ozekhome ya Kara da cewa zargin EFCC ba komai bane illa karya ba tare da hujjar cewa tsohon gwamnan ya karkatar da wadannan kudaden zuwa wani asusun sa na kashin kai.

Don haka a zahiri tsakanin 4 ga Mayu, 2018 zuwa yau 2 ga Satumba, tsohon gwamnan da ya yi wa jihar hidima ya tafiyar da ita bisa gaskiya yana fuskantar azaba mai tsanani da wahala na kusan shekaru hudu da rabi ba tare da ya aikata wani laifi ba a cewar lauyan

 “Amma a yau adalci ya fito, kotu ta gano cewa tsohon gwamnan bai saci Kobo a asusun gwamnatin Filato ba" inji Ozekhome.

A nashi bangaren Lauyan hukumar EFCC, Oluwaleke Atolagbe ya ce har yanzu ba su sami rubutaccen hukuncin ba amma da zarar sun samu za su sake duba hukuncin su ga ko akwai bukatar su daukaka kara.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci