OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

"An azabtar da ni saboda yakar cin hanci da rashawa," - Magu

AIG Ibrahim Magu| Photo Source: The Guardian

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu, ya bayyana cewa yakar cin hanci da rashawa ita tayi sanadiyar ficewar sa daga hukumar.

Mista Magu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja a wajen bikin karramawar da kungiyar dalibai mata ta Arewa ta shirya domin karrama shi.

"Yakar cin hanci da rashawa ne ya yi min sanadi,sai dai ina mai farin ciki dangane da yadda gaskiya ta fara bayyana kanta a irin abubuwan da suke faruwa a 'yan kwanakin nan," in ji shi.

Mista Magu wanda ya samu wakilcin dansa, Mohammad-Saeed Ibrahim-Magu, ya gode wa kungiyar da ta ba shi lambar yabo wato “Achiever per Excellence” ya bayyana farin ciki sa da samun wannan kyauta.

A’isha Nasir, mai magana da yawun kungiyar wacce ta kunshi dalibai mata na jami’o’i a sassan arewacin Najeriya, ta bayyana cewa sun zabi Mista Magu ne saboda sadaukar da kai ga bautar kasa.

“Yakar cin hanci da rashawa a Najeriya aiki ne mai matukar daure kai wanda yana bukatar amfani da siyasa ko abubuwan da ake so.

“Ku ƙaunace shi ko ku ƙi shi, Ibrahim Magu ya ya yaƙi cin hanci da rashawa zuwa matakin da ba a taba tunanin zai kai ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa kyautar ta zo ne bayan hukuncin da babbar kotun Abuja ta yanke a ranar 4 ga watan Oktoba wanda alkali Yusuf Halilu ya yanke

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci