OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Yanka Wani Mai Gadin Kasuwa A Jos

Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Yanka Wani Mai Gadin

Rundunar ƴan sandan Jos ta tabbatar da kama wasu mutum bakwai da ake zargin suna da hannu a kisan wani mai gadi.

 A ranar Asabar ne aka gano gawar mai gadin mai suna Muhammad Kabiru da aka yankansa a kasuwar Ultramodern a garin Jos.

Mahukuntan kasuwar sun ce marigayin wanda mai gadi ne a kasuwar an kashe shi ne da tsakar dare yayin da yake tsaka da aikinsa an tsinci gawar tasa a kusa da kasuwar.

Shugaban Kasuwar Alhaji Jamilu Kabiru, a lokacin da yake zantawa da Daily Trust game da lamarin, ya ce, “An kashe mana, daya daga cikin sananne kuma amintaccen mai gadin kasuwar mu.

“Daya daga cikin abokan aikina ne ya kira ni da safe ranar Lahadi yace in zo in ga gawar.

Tabbas wannan abun bakin ciki ne.

Mun kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

” Ya ce marigayin ya shafe tsawon shekaru 15 yana aiki kuma ba a taba samun matsala da shi ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu wajen aikata laifin.

Alabo ya ce, “DPO na yankin ya fara aiki kan lamarin.

Duba da yanayin yadda abin ya faru an kama wasu mutane bakwai da ake zargi.

Ana ci gaba da bincike har sai an gano gaskiyar lamarin."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci