OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane Takwas Sun Mutu a Hatsarin Mota a Jihar Filato

Mutane Takwas Sun Mutu a Hatsarin Mota a Jihar Filato

Aƙalla Mutane 8 ne suka mutu yayin da wasu biyu suka samu raunuka sakamakon wani hatsarin mota da ya afku a jihar Filato ranar Asabar.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa dake Jos, Peter Longsan ne ya tabbatar wa jaridar Punch.

A cewar sa, hatsarin motan ya afku ne a kan hanyar Jos zuwa Lamingo da yammacin ranar Asabar da misalin karfe 3:10 na rana.

“Hatsarin ya haɗa da motoci guda biyu, Toyota Hiace bas da wata mota kirar Honda Pilot.  

"Adadin mutanen da ke cikin motar sun kai 10, inda takwas suka mutu (maza uku, manyan mata hudu da yaro daya) yayin da wasu biyu suka samu raunuka.

“Hukumar ta kai mutanen biyu da suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos domin kula da lafiyar su.

“Wannan mummunan lamari ya faru ne a sakamakon yawan gudu da wani direba ya yi, wanda ya kai ga gagara shawo kan motar har ya yi karo da motocin biyu.”

Jami’in ya shawarci masu ababen hawa da su kiyaye yawan gudu, inda ya yi nuni da cewa, yawan gudun da ake yi shi ne ke haddasa mace-mace da munanan raunuka."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci